Ayatullah Muhammadu Hatami, da ya ke gabatar da hudubar Sallar Juma’a anan Tehran ya ce; A yayin tattaunawar da ta kai ga cimma yarjejeniyar Nukiliya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tabbatarwa da duniya cewa ba ta son kera makaman Nukiliya. Limamin ya kara da cewa; Wajibi ne ga al’ummar Iran din da su kasance a cikin fadaka daga makircin uwar shaidanu Amurka. Ayatullah Hatami ya ci gaba da cewa; Fiye da rabin karni Amurka ta yi taa cutar da al’ummar Iran, wanda shi ne musabbabi da al’ummar ta ke bada taken yin tir da Amurka. Dangane da ziyarar da jami’an gwamnatocin kasashen turai su ke kawo wa Iran, limamin ta Tehran ya ce; hakan yana nuni da yadda su ke da bukatuwa da shigowa kasuwannin Iran.288