26 Yuli 2015 - 17:06
Malam ya isa dakin taro, Sheikh Muhammad Asi daga Washington na jawabi

Yanzun haka dai rahotannin da suke iso mana sun tabbatar da cewa jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky ya isa dakin taro kuma daya daga cikin manyan bakin da aka gayyata Sheikh Muhammad Asi limamin Jummu'a na birnin Washington na Amurka yana gabatar da ..................,

Jawabin sa.

A lokacin jawabin nasa babban Malamin ya fara da gabatar da godiya ga Allah Ta'ala da salati ga Manzon sa [SAWA] sannan sai ya yi godiya ga wadan da suka shirya wannan gagarumin taro kuma suka bashi damar gabatar da jawabi.

Malami ya fallasa yahudawan Sahayoniya sosai a cikin jawabin nasa, yadda suke amfani da karya da yaudara wajen cimma burin su na duniya.

Haka nan Malamain yayi Magana kan yadda suka mamayi kasar Falasdinu da yadda suke ta ci gaba da aikata munanan aika-aika.

ga wasu 'yan hotunan da muka dauka a lokacin.288