A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar Hamas ta sanar da karya mafi muhimmanci a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi da ya haɗa da kai kayan agaji da sake samar da wuraren da 'yan gudun hijira, da kuma ka'idojin jin kai kamar haka:
1- Rashin ba da izinin shigar da manyan motocin mai guda 50 a kowace rana bisa yarjejeniyar da aka kulla, ta yadda a cikin kwanaki 42 motocin mai guda 978 ne kawai suka shiga yankin Zirin Gaza, inda a kullum a kalla manyan motoci 23 ke shiga yankin.
2- Kafa dokar hana shigo da man fetir iri-iri a yankin na zirin Gaza, duk kuwa da cewa yarjejeniyar ta yi nuni da cewa wannan lamari ya halatta.
3- Bayar da takardun izinin shigar da gidaje 15 tafi da gida ka kacal daga cikin gidaje 60,000 na tsararrun gini da aka amince da su, baya ga kuma an bayar da izini na shigar da tanti bakin gwargwado.
4- Hana shigar da manyan motoci da injuna da ake bukata domin kawar da tarkace da tono gawarwakin, ta yadda 9 daga cikin wadannan injuna ne kawai suka shiga yankin Zirin Gaza, yayin da wannan yanki na bukatar akalla 500 daga cikin wadannan injunan.
5- Hana shigar da kayan gini don sake gina ababen more rayuwa da asibitoci.
6- Hana shigar da kayan aikin likitanci da suka dace don bude asibitoci da barin motocin daukar marasa lafiya 5 kacal su shiga Zirin Gaza. 7- nuna adawa da shigo da kayan aikin da bangaren tsaron farin kaya ke bukata.
8- Hana kunna tashoshin samar da wutar lantarki da hana shigar da kayan aikin da ake bukata don sake ginawa da farfaɗo da wutar lantarki.
9- Hana shigar da kudade a bankunan zirin Gaza da kuma adawa da musayar kudaden da suka lalace.
Your Comment