Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sakatare Janar na Hizbullah na Lebanon da yake jaddada alhakin gwamnati na kiyaye iko da 'yancin kai na ƙasar ya ɗauki duk wani yunƙuri na kwance damarar Hizbullah a matsayin buƙatar Amurka da Sahyoniyawa kuma ya ce: Takaita makamai da wannan dabarar yana nufin lalata ikon Lebanon.
Da yake magana game da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Sahyoniyawa ta ke yi akai-akai, ya kira ayyukan ta’addancin gwamnatin bayan yarjejeniyar a matsayin ci gaba da kai harin keta iyka kuma ya jaddada cewa Hizbullah ba za ta miƙa wuya ga buƙatun Amurka da Isra'ila a kowane hali ba.
Your Comment