13 Disamba 2025 - 21:51
Source: ABNA24
IOM: Dubban Daruruwan Mutanen Da Suka Rasa Matsugunansu A Gaza Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Duniya ta yi gargadin a ranar Asabar cewa daruruwan dubban mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Gaza na fuskantar barazanar ruwan sama mai karfi, yayin da aka toshe hanyoyin shigar da kayan da ake bukata don gina matsugunansu da buhunanan yashi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cikin wata sanarwa, kungiyar ta ce kusan mutane 795,000 da suka rasa matsugunansu a yankunan da ke da tarkace, inda iyalai ke zaune a wuraren da ba su da aminci, suna fuskantar barazanar ambaliyar ruwa.

Hukumar IOM ta jaddada cewa an jinkirta shigar da muhimman kayan da za a iya amfani da su don karfafa matsugunansu, ciki har da itace, plywood, jakunkunan yashi da famfunan ruwa, zuwa Gaza saboda takunkumin da isra’ila ke ci gaba da sanyawa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha