11 Disamba 2025 - 13:52
Source: ABNA24
Isra’ila: Hizbullah Ta Dawo Da Ikonta Na Soja A Yawancin Yankunan Rikici

Jami'an Isra'ila sun yi gargadin cewa Hizbullah, tare da tallafin kuɗi daga Iran, ta sami nasarar dawo da ikonta na soja kuma yanzu tana ɗaukarta a matsayin barazana ta siyasar yaƙi ga Tel Aviv.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar Isra'ila Yediot Aharonot ta kawo bayanin daga manyan jami'ai Isra’ila cewa Hizbullah ta sami nasarar dawo da wani muhimmin ɓangare na ƙarfinta na soja a yankunan yaƙi daban-daban. Suna da'awar cewa hakan ya yiwu ne ta hanyar sake dawo da tallafin kuɗi daga Iran a cikin 'yan watannin nan.

Tel Aviv ta bayyana wannan yanayi a matsayin komawa ga matakin karfi da ya kasance kafin ƙaruwar rikicin yankin kuma ta yi gargaɗin cewa "jira zuw lokacin da ba’a anbata ba ba zai zamo mafita ba – wanda wannan wata alama ce a fili ta yiwuwar faɗaɗa ayyukan soja idan hanyoyin diflomasiyya suka gaza samar da sakamako mai ma'ana.

Wannan rahoton ya zo ne a lokacin da majiyoyin tsaron Isra'ila suka yi iƙirarin cewa goyon bayan Iran ga Hizbullah, wanda ya daɗe yana raguwa, ya fara ƙaruwa. Wannan ya bai wa Hizbullah damar sake gina tsarin makamai masu linzami da jagororinta da hanyoyin sadarwa da kuma rundunarta ta musamman, musamman rundunar Ridwan a yankunan arewa.

A wani binciken kuma, Yediot Ahronot, daga jami'ai a Tel Aviv ta ruwaito cewa Lebanon ta yi nasarar kwace kaso 80% na makamai a yankunan da ke kudancin Kogin Litani. Isra'ila ta yi ikirarin cewa wannan nasarar ta samo asali ne daga matsin lamba mai tsanani na diflomasiyya tare da hadin gwiwar Washington, Paris, da Majalisar Dinkin Duniya. Duk da haka, jami'ai sun amince cewa gwamnatin Lebanon ba za ta iya kammala aikin ba kafin karshen shekara saboda kalubalen siyasa da tsaro, da kuma rauninta a yankunan kudu masu mahimmanci.

Waɗannan batutuwa a sun zo ne bisa ga yanayin hare-hare a lokaci-lokaci da kuma rikice-rikicen da suka shafi iyaka tsakanin Lebanon da Isra'ila tun daga watan Oktoban 2023, wadanda ba su kai ga yakin basasa ba. A halin yanzu, Amurka, Faransa, da sauran masu ruwa da tsaki na kasa da kasa suna aiki don cimma yarjejeniya a hankali don hana babban rikici.

A cewar labarin Isra'ila, sake farfaɗowar Hizbullah a ƙarfin soja yana haifar da barazana ta dabarun diflomasiyya kaɗai - musamman idan aka yi la'akari da ci gaba da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da rokoki da ke kai hari kan sansanonin sojojin Isra'ila a Galilee da kuma ƙaruwar ayyukan tsaro na Hizbullah a arewacin Kogin Litani.

Waɗannan gargaɗin suna da alaƙa da aiwatar da kudurin Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701. Isra'ila ta yi iƙirarin cewa kudurin ya hana kasancewar mayakan Hizbullah a kudancin Lebanon, yayin da Lebanon ta dage cewa ita ma Isra'ila  ba ta bi wannan kudurin ba - musamman game da janyewa daga yankin Gonar Shebaa, sakin fursunonin Lebanon, da kuma dakatar da hare-haren sama na yau da kullun.

Masana sun yi imanin cewa waɗannan kalamai na jami'an Isra'ila wani ɓangare ne na ƙoƙarin siyasa na matsa wa ƙasashen duniya lamba don hanzarta warware rikicin kan iyakar Lebanon da kuma kafa sabon tsarin tsaro wanda zai tilasta wa Hizbullah ta koma cikin cibiyar yankin Lebanon.

Your Comment

You are replying to: .
captcha