Sojojin Isra'ila shirye da tankokin yaki da dama sun tunkari birnin Jenin a karon farko tun bayan intifada na biyu, yayin da ministan tsaron Isra'ila Katz ya umurci sojojin da su yi shiri na tsawon lokaci a sansanonin da suke kai hari a gabar yammacin kogin Jordan.
Kamal Abu Rabb, gwamnan Jenin, ya sanar da cewa a sa'i ɗaya kuma sojojin gwamnatin mamaya sun kafa dokar hana fita ta sa'o'i 48 a birnin Qabatiya na lardin Jenin.
