Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hassan al-Abadi, wakilin al'adu na Kataib Sayyidish Shuhada a Iran a taron kasa da kasa na "Shahidan Al-Aqsa; Daga Gaza zuwa Zariya" wanda aka gudanar bisa halartar manyan malamai, masu bincike, iyalan shahidai da masu fafutuka na fagen gwagwarmaya a haramin Sayyidah Ma’asumah (A.S.), yana mai nuni da abin da ya faru na kisan gillar da aka yi wa masu zaman makokin Imam Husain a Zariya, ya kira wannan lamari da "ci gaban kiyayyar tarihi ga makarantar Ahlul Bayt (A.S.)" inda ya ce: Kisan gillar masu makoki ranar 10 ga Muharram a Najeriya ba lamari ne na bazata ba, a'a wani bangare ne na tsohon tsararren aiki na bice hasken gaskiya.
Da yake karanta ayar "Kuma kada ku dauki wadanda aka kashe a hanyar Allah a matsayin matattu...", Al-Abadi ya kara da cewa: Shahidan Najeriya suna da rai kuma ba za a iya bice wannan jinin ba. Tun daga harin farko da aka kai wa Gidan Annabi har zuwa yau, makiya sun yi ƙoƙarin raunana Musulunci na gaskiya, amma sunnar Allah ita ce samar da tsira ga wannan makaranta da kuma wulakanta azzalumai.
Wakilin rundunar sojojin Sayyidush -Shuhada ya ci gaba da cewa: Muna gaya wa mutanen da aka zalunta da jarumai na Najeriya: Ba ku kaɗai ba ne. 'Yan'uwanku a Kataib Sayyidish -Shuhada a shirye suke su shiga da gaske don tallafawa gwagwarmayar Musulunci a Najeriya; ana iya cimma wannan goyon baya a kowane mataki - al'adu, zamantakewa, da kafofin watsa labarai.
Ya jaddada cewa: Kowane digo na jini da aka zubar a Zariya nauyi ne na alhakinmu kuma la'ana ce ta har abada ga makiya.
Abadi ya yi gargaɗi ga masu aikata wannan laifi: Ku yi duk abin da za ku iya; ku gabatar da dabarunku da ƙoƙarinku, amma ba za ku iya kashe tunawa da Ahlul-Bait (AS) ba, kuma ba za a goge kunyar wannan laifi daga kanku ba. Kwanakinku suna da iyaka, kuma alkawarin Allah na wulakanta azzalumai tabbas ne.
Your Comment