Kafofin yada labarai na ƙasa da ƙasa sun maida hankali wajen watsa taron jana'izar Sayyid Hasan Nasrallah Da Sayyid Safiyuddin shugabannin kungiyar Hizbullah.
A daidai lokacin da ake jana'izar shahidan Sayyid Hassan Nasrallah da Sayyid Hashim Safiyuddin, kafafen yada labarai na duniya sun yi ta watsa wannan gagarumin taro da ba shi da misali.
Shafin yanar gizo na Rossiya Al-Youm ya bayar da rahoton yadda jama'a suka hallara a wajen jana'izar shahidan Sayyid Hassan Nasrallah a birnin Beirut, inda ta sanar da cewa tun da sanyin safiyar yau dubban magoya bayan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ne suka hallara a wani babban filin wasa na birnin Beirut domin halartar jana'izar Sayyid Hassan Nasrallah.
Andrey Alexandrovich Pfefelov, dan jarida kuma editan gidan talabijin na Roz da ke kasar Rasha, ya ce: "A yau, ni da duk wadanda ke bankwana da Nasrallah, ina taya su cikin bakin ciki da damuwa".
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya rubuta cewa: Nasrallah ya kasance shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon sama da shekaru 30 kuma daya daga cikin wadanda suka kafa ta, wanda ke da tasirin gaske a tsakanin kungiyoyi a yankin. Ana girmama shi sosai a cikin gwagwarmaya bisa jagorancin Iran.
Shafin yanar gizo na France 24 ya bayyana jana'izar gawawwakin shahidan "Sayyid Hassan Nasrallah" da "Sayyid Hashim Safiyuddin" a matsayin wata alama ta nuna karfin Iran da Hizbullah.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, dubun dubatan mutane ne suka taru a Dahiyat birnin Beirut domin nuna girmamawa ga shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah.
Kamfanin dillancin labaran jaridar New York Times ya kawo cewa, an gudanar da jana'izar ne a babban filin wasan motsa jiki na kasar Lebanon da ke yankin kudancin babban birnin kasar, wanda aka kawata shi da manyan hotunan shahidi Nasrallah mai hawa biyu da kuma take mai nuni da ci gaban gwagwarmaya
Jaridar Al-Nahar: Jana'izar Nasrallah da Safiuddin ta kasance abar tunawa a jana'izozi mafi girma a duniya.
Jaridar Al-Nahar ta kasar Lebanon mai alaka da kungiyoyi goma sha hudu na Maris ta bayyana jana'izar Sayyid Hasan Nasrallah Da Sayyid Hashim Safiyuddin a matsayin daya daga cikin manyan jana'izar da aka yi a duniya.
Jana'izar Sayyid Hassan Nasrallah, tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah, da Sayyid Hashim Safiyuddin, a cikin dimbin jama'a, yana tuna irin fage na jana'izar da yankin gabas ta tsakiya da duniya baki daya suka shaida.
