Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul Bayt (AS) – ABNA – ya habarta maku cewa: An gudanar da taron
cika shekaru 9 da kisan kiyashi a Zariya, inda sojojin Nijeriya suka yi wa
mabiya Hujjatul Islam Wal Muslimen, Sheikh Ibrahim Zakzaky, jagoran Harkar
Musulunci ta Nijeriya (IMN) kisan kiyashi a watan Disamba 2015, an gudanar da
shi daga ranar 12 zuwa 14 ga Disamba.
A jawabinsa na rufe taron, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya jajantawa duk wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan lamari. Ya bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata suna da wasu munanan dalilai na murkushe harkar Musulunci da kuma kai masa hari da kansa, inda suka aiwatar da irin wannan kisan kiyashi.
Shaikh Zakzaky ya kuma yi nuni da yadda gwamnatin Najeriya ta yi watsi da doka da hakkin dan Adam wajen murkushe mabiya kungiyar. Ya yaba da gwagwarmaya da tsayin dakan da mabiya Harkar Musulunci suka yi duk da matsin lamba da zalunci da suka sha a hannun gwamnati da jami’an tsaro.
Ya yi tsokaci kan ikirarin haramta kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) da cewa wannan suna da gwamnati ta sanya wa harkar bai halatta b aba akan doka yake ba. Shaikh Zakzaky ya jaddada cewa "ba za a iya haramta harkar addini bisa ka'ida da hankali ba".
Idan dai ba a manta ba, kisan kiyashin da ake magana a kai ya faru ne a ranar 12 ga watan Disamba, 2015, a lokacin da sojojin Najeriya suka kai wa ‘yan Shi’a hari a Zariya, inda suka kashe da jikkata wasu da dama. Harin ya kai ga rushe Hussainiya Baqiyyatullah (AS) tare da kashe wasu manyan jami’an Harkar Musulunci.