22 Mayu 2024 - 10:47
Ismail Haniyah, Shugaban Ofishin Siyasa Na Hamas, Ya Gana Da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci + Hotuna Da Bidiyo

A wannan ganawar, Haniyah ya ce ina mika ta'aziyyata ga mai girma da kuma 'yan uwa na Iran da mahukuntan kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh a ganawa da ya yi da jagoran juyin juya halin musulunci a yau a madadin gwamnati da al'ummar Palastinu, ya jajantawa Ayatullah Khamenei da al'ummar Iran bisa wannan rashi da aka samu na shugaban kasa da ministan harkokin waje da Abokan tafiyarsa.

Yace a wani bangare na wannan ganawar: Na tabbata Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da ba wa al'ummar Palastinu goyon baya domin mu daga tutar tauhidi da cin nasara a kan Qudus mai tsarki.