Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto maku daga Kamfanin dillancin labaran reuters in da majiyarsa ta nakalto daga kafafen yada labaran kasar Siriya sun sanar da cewa an ji karar fashewar wani abu a birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya. Ba a bayar da karin bayani kan wannan batu ba, amma galibi a irin wannan yanayi, ana sanar da karar fashewar wasu abubuwa a cikin sa'o'i na safe a Damascus da kewayen wannan birni, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da mayakan yahudawan sahyoniya suka yi.
13 Agusta 2023 - 05:03
Lambar labari: 1386623
An ji karar fashewar wani abu a birnin Damascus, babban birnin kasar Siriya