Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Laraba, Ashed ya sanar da murabus din nasa, yayin da yake magana kan tsoma bakin siyasa na bangaren dama da 'yan majalisar ministocin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wadanda suka bukaci a dauki tsauraran matakai kan masu zanga-zangar adawa da Netanyahu.
Duk da cewa Itmar Ben Goyer, ministan tsaron cikin gidan gwamnatin sahyoniyawan, shi ne ya bukaci a dauki kwakkwaran mataki kan masu zanga-zangar da suka rufe tituna da manyan tituna domin nuna adawa da sauye-sauyen shari'a na Netanyahu, babban jami'in 'yan sandan Tel Aviv bai ambace shi ba a cikin sanarwar nasa.