31 Agusta 2022 - 19:30
Dakarun Hashdu Sha’abi Na Iraki Sun Sanar Da Kashe Wani Kwamanda A kungiyar Ta’adda Ta ISIS

A wani faramaki da dakarun na Hashdush sha’abi suka kai a yankin musel babban birnin lardin Nainawa suna samau nasarar kashe wsu yayan kungiyar ISIL ciki har da wani babban kwamandanta a yankin

A gefe guda kuma kungiyar ta Hashdush sha’abi ta sanar da kashe mamabobinta 4 tare da jikkata wasu sakamakon fashewar wani Bomb a Arewacin birnin Bagadaza lamarin ya faru ne bayan fashewar bomb a Wani wuri da suke gudanar da ayyukan share yankin Tarmiyah daga geron kungiyar ta’adda ta ISIL

A watan Decemba shekara ta 2017 bayan shekaru 3 da rabi ana yaki da kungiyar Yan Ta’adda ISIS inda suke rike da kashi 3 na kasar , gwamnatin kasar ta Iraki ta sanar da yantar da dukkan yankunanta daga hannun yan ta’adda na ISIL

Sai dai har yanzu akwai sauran geron yan ISIL da suke ci gaba da kai hare-hare a gefen biranen Bagadaza saladin diyala Kirkuk Nineveh da kuma lardin Anbar.

342/