Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - mininstan harkokin cikin gida bangaren abin da ya shafi tsaro Majid –Ahamadi a sa’ilin ganawarsa da Robert Mardini babban darakatan kungiyar ta Red Cross ya fadi cewa Akalla iran ta karbi yan gudun hijirar kasar Afghnistan sama da miliyan biyar a kasarta, wadanda suka tsere daga kasar bayan da kungiyar taliban ta karbe iko da mulki a kasar ,
Adaidai lokacin da yakin kasar Ukrain yake barazana game da samar da Abinci a duniya, yada iran take fuskantat kalubale wajen samar da Alkama ga Alummar kasarta, yace Afghanawa dake rayuwar a kasar Iran suna samun Tallafin dala biliyan 5 a duk shekara, kuma an yi musu Allurar rigakafi miliyan 4.5 daga lokacin bullar cutar Annobar Korona Virus zuwa yanzu.
Babban darektan na red Cross yanzu haka yana ziyara ne a kasar Iran a lokacin bukin cika shekaru 100 cur da kafa hukumar Bada Agaji ta kasa da kasa wato Red Cross , yace Iran tana yin abin da ya dace da take barin Afghanawa suna shiga kasarta, kuma ya godewa Iran game da kokarin da take yin a tallafawa yan gudun hijiran kasar Afghnistan.
342/