Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A kwanan nan ana dai cikin zaman dar dar a yankunan Falasdinawa da Isra’ilar ta mamaye musamman a garin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da firaministan Isra'ila Naftali Bennett ya baiwa dukkan jami'an soji da na tsaro cikakken 'yancin gudanar da ayyukansu a yankunan, furucin da ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta dauka a matsayin umarni na kashe Falasdinawa.
Game da halin da ake ciki a yankin MDD ta bakin Babban sakatarenta Antonio Guterres, ya nuna matukar damuwa game da halin da ake ciki na ruruwar wutar rikici tsakanin Faladina da Isra’ila.
342/