24 Maris 2022 - 16:59
Hare Haren Al'Shabab Sun Kashe Mutum Sama Da 30 A Somaliya

Hukumomi a Somaliya sun ce sama da mutum talatin ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare hare biyu da suka faru a tsakiyar kasar, da yammacin ranar Laraba, kamar yadda wani jami’in ‘yan sanda ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.

Har yanzu ana cikin tattara alkaluman wadanda lamarin ya rusa dasu a harin na biyu da aka kai da mota a cewar Isak Ali Abdulle.

Kafin nan rahotanni sun ce daga cikin wandanda lamarin ya rusa dasu har da wata 'yar majalisar kasar Somaliya, yayin hare-haren a garin Beledweyn na tsakiyar kasar.

Firaminista Mohamed Hussein Roble ya bayyana kashe Amina Mohamed Abdi a matsayin "kisan gilla". Shi kuma shugaban kasar Abdullahi Farmajo ya aika da sakonsa na ta'aziyyar ta Twitter:

Kungiyar Al-Shabab dai ta dauki alhakin kai hare-haren - wadanda aka kai a biranen Mogadishu da tsakiyar Beledweyne.