Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Annashr ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a wani taron da ya yi da manya-manyan jami’an kungiyar a birnin Beirut a safiyar yau Laraba.
Sayyid Nasarallah ya ce muna bukatar dukkan kawayemmu su sami nasara a zaben 15 ga watan Mayu mai zuwa don nasaransu ita ce nasararmu. Ya kuma kara da cewa zaben majalisar dokokin kasar Lebanon mai zuwa shi ne zabe mafi muhimmanci da kuma hatsari a tarihin siyasar kasar, ganin irin yadda makiyan kasar suka sa kungiyar da kawayenta a gaba.
342/