12 Maris 2022 - 13:37
Bayan Harba Tauraron Dan Adam Na “ NUr-2” Iran Ta Ce; Takunkuman Da Aka Kakaba Mata Ba Za Su Hana Ta Cigaba Ba

Kwamandan dakarun kare juyin musulunci wanda yake kula da shirin sararin smaniya na Iran, Janar Ali Ja’afa Abady ya bayyana cewa; An harba tauraron dan’adam na “ Nur Na 2” cikin nasara, wanda hotunan da yake aikowa sun fi “ Nur Na 1” karfi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shi ma ministan harkokin wajen Iran Husain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa; Bisa samun dace daga Allah madaukakin sarki, masana na Iran da dakarun kare juyin musulunci, sun harba tauraron dan’adam Nur- 2 cikin nasara ta hanyar makami mai linzami samfurin “Qasid” da shi ma kirar Iran ce.

Amir Husain Abdullahiyan ya cigaba da cewa; Babu yadda za a yi wani takunkumi ya kawo wa al’ummar Iran ma’abociyar jihadi, tasaiko akan tafarkinta na cigaba.

A jiya Laraba ne dai janar Ja’afar Abady ya sanar da harba tauraron dan’adam din cikin nasara.

Daga cikin ayyukan tauraron dan’adam din da akwai bibiyar kai da komowar abokan gaba, da kuma sauyin yanayi.

342/