Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Muhammad Bakir Kalibaf wanda ya gana da takwaransa na kasar Pakistan, Kasim Khan Sury, ya yi ishara da alaka mai girma da take a tsakanin kasashen biyu sannan ya kara da cewa;
“ Iyakar kasashen biyu tana da tsawon gaske,don haka yin aiki tare a tsakaninsu ta fuskar tsaro yake da muhimmanci, kuma wajibi ne akan gwamnatocin kasashen biyu da kwamitocin majalisunsu, da su bunkasa alakar da take a tsakaninsu.”
Shugaban Majalisar Shawarar Musuluncin ta Iran ya kuma yi ishara da takunkumin Amurka akan Iran, wanda ya bayyana akan cewa na zalunci ne, don haka da akwai bukatar a karfafa alaka a tsakanin bangarorin biyu.
342/