Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahian da ministan kula da hanyoyi da sufuri Rostam Ghasemi da ministan makamashi ne suka sanya hannun a yarjeniyoyin,
A jiya litinin ne shugaban Iran Ibarahim Ra’isi ya isa babban filin saukar jiragen sama na kasar Qatar dake birnin Doha inda ya samu kyakkyawar tarba daga sarkin Qatar Tamin bin Hamad Al thani.
Shugaban ya isa kasar Qatar ne bisa gayyatar da sarkin Qatar yayi masa a hukumance kuma zai halarci taron shuwagabannin kasashen dake fitar da iskar gasa da za’a yi a kasar,
A taron manena labarai na hadin guiwa da shuwagabannin kasahen biyu suka yi a birnin Doha sun bayyana babban hadafin dake gabansu wato bunkasa dangantakar dake tsakaninsu a matsayinsu na yan uwa kuma makwabtan juna , da kuma halartar taron kungiyar kasashen masu fitard a iskar gas.
342/