6 Faburairu 2022 - 18:51
Iran: A Shirye Muke Mu Ci Gaba Da Tattaunawa Da Saudiya Cikin Mutunci

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasar Saudiya har zuwa lokacinda zasu kai ga fahintar juna.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta “Khabar” a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake zantawa da wayar tarho da firai ministan kasar Iraki Mustafa Al-Kazimi a jiya Asabar.

Sayyid Ibrahim Ra'isi ya kuma godewa kasar Iraki a shiga tsakani da take yi tsakanin kasashen biyu. Sannan ya bukaci gwamnatin kasar Iraki ta yi abinda zata iya yi don ganin an dakatar da yaki a kasar Yemen.

Daga karshen shugaba Raisi ya kammala da cewa kasar Iraki tana da matsayi na musamman a wajen Jumhuriyar Musulunci ta kasar Iran. Don haka a cikin shirinta na kwautata dangantaka da kasashe makobta, kasar Iraki tana da matsayi na musamman wajen hulda da ita.

A nashi bangaren firai ministan kasar Iraki Mustafa Al-Kazimi ya bayyana cewa kasarsa tana son ganin an kara dankon zumunci a tsakananin kasashen biyu a dukkan bangarori.

342/