Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar Alfurat News ta bayar da rahoton cewa, Ayatollah Sayyid Ali Sistani Babban malamin addinini na kasar Iraki ya fitar da wani sako inda ta bayyana wafatin Ayatullahi Safi Golpayegani a matsayin babban rashi tare da cewa: Ya kasance daya daga cikin masu kyawawan halaye addini abin koyi kuma daya daga cikin masu hidima ga addini.
Ga matanin sakon kamar haka:
Labarin wafatin babban malami bawan Allah Ayatullah Haj Sheikh Lotfollah Safi Golpayegani ya haifar da bakin ciki a zukantanmu.
Rasuwar wannan ma'abocin daraja, wanda ya kasance daya daga cikin malaman makarantar hauza ta Qum da kyawawan halayensa abin koyi, hakika babban rashi ne.
Ina mika sakon ta'aziyya kan wannan rashi mai raɗaɗi zuwa Sahibul Asr, da malamai tare da yin ta'aziyya ga 'yan uwa da sauran iyalansa, Allah ya jikansa da rahma.
342/