Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A ranar Lahadin da ta gabata, Kungiyatar ta ECOWAS ta amince ta rufe kan iyakokin Mali da kasashen yankin Sahel, sannan ta kara lafta mata takunkumin hana ta kasuwanci.
Tuni Faransa ta fito fili ta goyi bayan matakin da ECOWAS ta dauka a wani zama da ya gudana a zauren Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkiin Duniya.
Kungiyar ta ECOWAS ta kuma amince ta yanke tallafin kudaden da ake bai wa Mali tare da daskarar da kadarorinta a babban bankin kasashen yammacin Afrika da kuma sallamar jakadodinta na kasashen yankin Sahel.
Duk da cewa, shugaban mulkin sojin na Mali ya caccaki wadannan matakai, amma ya ce, kasar a shirye take ta yi sulhu da ECOWAS.
Wannan na zuwa ne bayan sojojin na Mali karkashin jagorancin Assimi Goita sun bayyana cewa, da yiwuwar a dauki tsawon shekaru biyar kafin su shirya zabe domin mika mulki lga farar hula.
342/