Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan bayanin ya fito ne yayin wata tattaunawa da ta wakana tsakanin jakadan faransa a Teheran, da kuma sakatare na majalisar ‘yancin dan adama da kuma shari’a ta Iran.
Jami’in na Iran Gharibabadi, ya kara da cewa tattaunawa ta kwararu kan sha’anin sharia’a za ta iya taimakawa kasashen wajen yin kyakyawar alaka a tsakaninsu.
Saidai ya soki lamirin wasu kasashe masu harshen damo game da batun hakkin dan adam, ya kara da cewa tattaunawa ita ce mahiyar hanya domin ciyar da batun kare hakkin dan adama a gaba amma kuma basu da wata alaka da siyasa.
Ya ce dokokin Iran da sharidodin iran duk sun tanadi bunkasawa da kuma mutumta hakkin dan adam.
Shi kuwa a nasa bangare jakadan Philippe Thiébaud, ya bayyana wasu ayoyi da suka shafi ‘yancin dan adam, tare da jinjinwa shawarwarin iran na musayar bayanai ta fuskar shari’a.
342/