21 Disamba 2021 - 13:22
​Najeriya: An Kashe Wasu Karin Mutane 38 A Jihar Kaduna

Bayan rahoton hare-haren da aka kai a kauyen Idasu,na karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, jami’an tsaro a jihar sun kara bada labarin kissan mutane 38 a kauyuka 3 a harin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Jaridar Nagerian tribune ta nakalto kwamishinan tsarin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Arwan yana fadar haka a jiya Lahadi. Arwan ya kara da cewa an gano sunayen mutane 29 cikin wadanda ‘yan bindiga suka kashe amma sauran har yanzun ba’a bada sunayensu ba.

Labarin ya kara da cewa sunayen mutanen da aka kashe a harin na Idasu da wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Giwa sun hada da Rabi`u Wada, Salisu Boka, Alh Nura Nuhu, Alh Bashari Sabiu, Alh Lawal Dahiru, Abbas Saidu, Inusa Kano, Mallam Lawal Nagar gari, Malam Aminu, Lawal Maigyad, Alh Mustapha, Lawal Aliyu, Sale Makeri, Sani Lawal da Auwal Umar.

Sauran sun hada da Jamilu Hassan, Badamasi Mukhtar, Malam Jibril, Lawal Tsawa Sule Hamisu, Sadi Bala, Kabiru Gesha Abubakar Sanusi, Saiph Alh Abdu, Haruna Musa, Lawal Hudu, Malam Shuaibu Habibu, Malam Yahaya Habibu, da kuma Abubakar Yusuf. Rahoton ya kammala da cewa akwai karin bayani dangane da hare-haren nan gaba.

342/