15 Disamba 2021 - 13:45
Ana Samun Ci Gaba A Tattaunawar Da Ake yi Tsakanin Iran Da Hukumar Nukiliya

Kakakin ma’ikatar harkokin wajen kasar Iran ya fadi cewa: tattaunawar da ake yi tsakanin Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran da darakta janar na hukumar nukiliya ta duniya Rafael Gross ana samun ci gaba sosai kan batutuwa daban –daban da ke da sarkakiya kan shirin ta na nukiliya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Eslami ya shaidawa manema labarai a gefen taron na birnin Tehran cewa hadin kai tsakanin Iran da hukumar nukiliya ta duniya ya takaita ne ga iyakokin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da kuma jarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi wato NPT

Ya kara da cewa: “idan hukumar ta IAEA tana son gudanar da bincike a cibiyar nukiliyar ta bisa yarjejeniyar nukiliya da aka cimma matsaya a kai a shekara ta 2015, to dole ne dukkan sauran bangarorin da ake tattaunawar da su su cika nasu Alkawuran,

Yace: “idan dai ba za su yi aiki da alkawuransu ba, kuma za su ci gaba da sanya wa Iran takunkumin zalunci da rashin Adalci, to bai kamata su neman tilastawa Iran ta basu hadin kai da suke bukata ba.

342/