14 Disamba 2021 - 18:53
Mutane 22 Sun Mutu 30 Sun Jikkata Sanadiyar Barkewar Rikicin Kabilanci A Kamaru.

Rahotanni suna bayyana cewa Al’ummomi a garin Kousseri dake Arewacin kasar Kamaru na ci gaba da yin gudun hijira zuwa kasar Chadi domin gujewa rikicin kabilanci da ya Addabi yankin , inda ya zuwa yanzu yayi sanadiyar mutuwar mutane 22 tare da jikkata fiye da 30 kamar yadda baban kwamishiniya a hukumar kula day an gudun hjira ta Majalisar dinkin duniya ta bayyana.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Rikici tsakanin makiyaya da masinta da ya samo asali kan wanda ke da ikon yin amfani da ruwa da wasu filaye a ranar 5 ga watan Decemba a kauyen Kousseri ya tilastawa sama da mutane 30,000 tserewa daga gidajensu ba shiri, zuwa kasar Chadi

Tun a ranar Alhamis da ta gabata ce aka aike da jami’an soji zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya, da dakile yi w uwa sake afkuwar rikicin , sai dai har ayanzu a kwai fargaba da ake da ita inda har yanzu kasuwanni da wajejan cin abinci sun kasance a rufe, bayan da aka kona wasu daga cikinsu a lokacin rikicin a kauyen Mousgoum tsakanin masinta dad a kuma yan kabilar shuwa Arab da suka kwashe dubban shekaru suna rayuwa a wajen.

Kimanin yan kasar Kamaru 20,000 yanzu haka suke gudun hijira a kasar Chadi wanda sama da 8500 har yanzu suna nan basu koma gidajensu ba sakamon sake barkewar rikicin.

342/