Kamar Yadda Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - ya bada rahoton cewa Jami'in al'adu na Kasa sake gina Haramomi masu tsarki ya bayyana cewa: Za a bude farfajiyar Sayyida Fatimah Zahra (a.s) a cikin Harmi mai tsarki na Imam Amirul Muminin Ali (AS) a daidai lokacin da aka haifi wannan babbar mace a Musulunci.
"Milad Jawadi" a cikin birnin Semnan ya sanar da bude farfajiyar Sayyida Fatimah Zahra (a.s) a watan Bahman shekara ta 1400 kuma ya kara da cewa: Wannan farfajiyar tana kusa da tsohuwar farfajiyar hubbaren Sayyidina Ali (AS) kuma dukkan ayyuka - ban da gidan kayan gargajiya. - nan da wata biyu Za a bayar dasu don fara anfani dasu.
Jami'in kula da harkokin al'adu na helkwatar da ke kula da sake gina wuraren ibada na kasar ya bayyana cewa: Za'a kammala simintin ginin farfajiyar gidan Sayyidah Zainab (AS) a daidai lokacin da aka haife ta itama kuma za a fara aikin anfani dashi.
Ya bayyana cewa hedkwatar sake gine gine ta na Hubbarori masu tsarki ta kammala ayyukan sake gina wurare har guda 180 tun daga farkon aikinta kuma a halin yanzu tana kan aiwatar da tsare-tsare, hedkwatar tana daukar matakai.
Jawadi ya sanar da karin kashi 30% na alkawuran da mutane suka dauka na taimakawa wajen sake gina Haramomin sannan ya ce: aiwatar da ziyarori na wqkilci ta hanyar yin rajista a shafin da kuma sadarwar bidiyo kai tsaye tare da hubbaren Imam Husaini (AS) a daren Juma'a da suka hada da ayyukan al'adu na helkwatar sake gina harami mai tsarki wanda mutane suka samu karbuwa sosai a cikin shekarar da ta gabata.
Ya kamata mu anbaci cewa "Babban aikin farfajiyar Sayyida Fatimih Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta)" wani zane ne na gine-ginen Musulunci, kuma daya daga cikin manyan ayyukan injiniya na farar hula a tarihin haramin. Wanda ya tsara wannan aiki, wanda ya aiwatar da shi kuma ya kafa wannan aiki shi ne "Hedikwatar sake gina wuraren ibada da haramomi" a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda aka kammala ta cikin cikakken hadin gwiwa tare da asusun bayar da taimako na yan Shi'ar Iraki da kuma yankin mai tsarki na Alawi a cikin 'yan shekarun nan.
farfajiyar gidan Sayyida Fatemeh Zahra (a.s) mai fadin sama da murabba'in mita 60,000, ya ninka girman tsohuwar farfajiyar harami mai alfarma kuma ya kunshi benaye 4 da manyan barandodi da dama. Baya ga wuraren ibada da na ziyara aikin ya hada da gina gidan tarihi da dakin karatu (mai daukar litattafai miliyan daya da kuma hade da wani babban dakin taron bita na maido da rubutun hannu) da kuma wani katafaren cibiyar koyar da karatun hauza da laccoci na addini. Wani katafaren dakin ibada gidan baki na alhazai, bandaki da dakin cin abinci na ma'aikatan dakin su ne sauran sassan wannan farfajiyar.
342/