Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Xin Ping ya ce gwamnatinsa za ta bada gudunmawar allurar rigakafin guda miliyan 600 kai tsaye, a yayin da saura miliyan 400 kuma za su fito daga wasu bangarori ne kamar saka hannun jari a bangaren samar da kayayyaki da ake da karanci a nahiyar Afrika. Kasar China dai ta sanya dinbim hannun jari a nahiyar Afrika kuma ita ce babbar kawar kasuwancin nahiyar Afrika. Inda take huldar kasuwanci da ya kai dala biliyan 200 a nahiyar a shekara ta 2019, kamar yadda ofishin jakadancin kasar China a Dakar ya bayyana.
Ya zuwa yanzu dai kasar China ta bada miliyoyin gudunmawar alluran riga kafin cutar kirar cikin gida wacce kamfanin magunguna na Sinopharm ta mikawa wasu kasashen Afrika marasa galisu daga lokacin bullar annobar.
342/