Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta kasar Rasha RT ta bayyana cewa ministocin harkokin waje na kasashen larabawa na gabas ta tsakayi da dama ne suka halarci taron.
Ana gudanar da taron na farfado da kasar Libya ne watanni 2 kacal kafin a gudanar da zaben shugaban kasa wanda ake saran zai sanya kasar kan turban hadin kai da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa.
Tun shekara ta 2011 ne kasar Libya ta shiga yakin basasa bayan kisan da yan tawaye masu samun goyon bayan kasashen yamma suka yiwa tsojon shugaban kasar Mu’ammar kazzafi.
342/