Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bangarorin sun tattauna game da halin da ake ciki a Aghanistan da yaki da ta’addanci da yarjejeniyar nukiliyar Iran, da kuma batun musayar fursunoni na tsakanin Amurka da kuma Iran.
Game da batun Afghanistan, Amir Abdollahian, ya yi kira ga MDD, data dubi halin da ake ciki a Aghanistan, sannan ya bukaci MDD, data dauki matakai masu tsauri domin yaki da kuma kawo karshen ayyuka ta’addanci a Aghanistan.
Ya kuma nan gaba Iran za ta karbi bakunci wani taron na makobtan Aghanistan domin tattauna halin da ake ciki.
Game da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran kuwa, ya ce tattaunawar data wakana tsakanin kamamin ministan harkokin wajen Iran, da mukadashin mai kula da harkokin waje na kungiyar tarayyar turai, Enrique Mora, a Tehran, ta yi armashi, kuma za’a ci gaba da tattaunawa nan gaba.
A gefe guda kuma da ya tabo batun musayar fursunoni tsakanin Iran da AMurka, Amir Abdollahian, ya ce, wannan aiki lamari na jin kai, amma bai dace ba a rika sanya wannan batu a cikin tattaunawar nukiliyar Iran.
A nasa bangare babban sakataren na MDD, ya yi fatan tattaunawar ta nukiliyar Iran, za ta haifar da da mai ido, tare da shan alwashin aikewa da kayan tallafi a kasar Afghanistan.
342/