Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na ‘Afrianews’ ya bayyana cewa wakilai daga bangarori daban –daban na kasar kimani 1,600 suka zabi Gbagbo a matsayin shugaban sabuwar jam’iyyar wacce aka sanyawa suna “The African People's Party's congress,(PPA-CI) .
Labarin ya kara da cewa, baki daga wasu jam’iyyun siyasa daga wasu kasashen Afirka sun sami halattar taron kaddamar da jam’iyyar a birnin Abidjan babban cibiyar kasuwancin kasar a jiya.
Kafin haka dai Gbagbo, ya rike shugabancin kasar ta Ivory Coast daga shekara 2000-2011, a lokacin da aka tube shi da karfi bayan ya ki amincewa da sakamakon zaben da ya bawa shugaban kasa mai ci, wato Alhasan Watara nasara. An kashe mutane kimani 3,000 a rikincin da ya biyu bayan zaben.
Daga karshe an kai Gbagbo zuwa kotun kasa da kasa da ke birnin Hugue, wacce ta wanke shi daga aikata wani laifi daga baya.
342/