Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan dai ita ce tafiya ta farko da shugaban kasar Iran na 8 ya kai zuwa kasashen waje tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Iran a watan Augustan da ya gabata. Haka zalika bayan halartar taron kasashen Shanghai zai gana da manyan jami’ai da jakadun kasashen da ke halartar taron koli na SCO
Daga karshe an nuna cewa bayan halartar taron na kasashen Shanghai zai gana da takwaransa na kasar Tajikistan inda za su tattaunawa kan hanyoyin da kasashen biyu za su bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu
Daga cikin abubuwa da zai gudanar ayayin ziyarar tashi zai gana da iraniyawa dake zaune a kasar ta Tajikistan.
342/