Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : wanda ya rawaito labarin, ya ce, Isra’ila ta bude hanyar shiga Kerem Shalom a wanna Laraba, haka kuma ta fafada wuraren kamun kifi a yankunan Falasdianwa dake karkashin ikon Hamas.
Duk da cewa hukumomin na Isra’ila basu yi karin haske ba game da dalilin sassauta matakan, amma hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata ganawa da akayi tsakanin shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da kuma ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz a birnin Ramallah.
Yayin ganawar da akayi a lokacin, bangarorin sun tattauna kan batutuwan da suka shafi inganta tsaro da tattalin arziki a Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza, da alkawarin ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.
Ganawar kuma ta zo ne bayan ziyarar da firayi ministan Isra’ila Naftali Bennett, ya kai a birnin Washington, inda ya gana da shugaban Amurka Joe Biden.
342/