31 Agusta 2021 - 10:05
​Iran Ta Gudanar Da Juyayin Shahadar Ali Rajai Da Bahonar Da Kuma Raya Ranar Yaki Da Ta’addanci Ta Kasa

A yau litinin ce aka gudanar da taron girmama tsohon shugaban kasar Iran shahid Mohammad Ali Rajai da kuma firai ministansa shahid Mohammad Javad Bahonar, wacce kuma ita ranar yaki da ta’addanci ta kasa a nan Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya bada rahoton cewa an gudanar da taron tunawa da kuma girmama wadanna shahidai ne a wurin da suka yi shahada a kudancin Tehran, a ranar 30 ga watan Augustan shekara 1981 shekaru 40 da suka gabata.

Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan Iran a shekara 1979 ‘yan ta’adda su fara kashe jami’an gwamnatin kasar, kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda suka hada da kungiyar MKO ko Mujahidun Khalkh ne suka gaba a wannan ta’asar. MKO dai a halin yanzu ta na samun kariya daga kasashen yamma karkashin tutar wadanda aka zalunta.

Kungiyar ta sha kai hare-hare kan fararen hula da jami’an gwamnatin JMI, daga ciki har da dana bom da tada shi a ofishin firai ministan kasar Iran na Lokacin wanda ya kai shahadar mutane da dama daga ciki har da shi shugaban kasa Ali Rajai da firai ministansa Bahonar.

Mai maga a taron tuna wadannan shahidai a yau Litinin, mataimakin shugaban kasa a kan al-amuran majalisar dokoki Mohammad Hussain ya bayyana cewa kungiyar munafukai ta MKO ta kashe mutane kimani 17,000 a kasar Iran.

342/