Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto majiyar tana cewa kamfanin google ya shafe muhimman kayakin aiki na yanar gizo wadanda suka hada da Rubika da kuma wadanda ake yawan amfani da su.
Cibiyar ta kara da cewa wannan matakin da kamfanin google ya dauka zai shafi harkokin kasuwanci na kananan masana’antu da dama a kasar, kuma yin hakan take hakkin Iraniyawa ne na amfani da babban shafin bincike na google.
Daga karshe labarin ya kammala da cewa cibiyar za ta hada kai da ma’aikatar sharia da kuma ma’aikatar harkokin wajen kasar don bin kadin Iraiyawan da suka cutu sanadiyyar wannan aikin.
342/