Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Abbas Fallah mataimakin shugaban gudanar da wasannin ya na cewa ana gudanar da wasannin ne a birnin Shahinshar na lardin Esfahan. Kuma manufar gudanar da wasannin ita ce samar da zaman lafiya, kulla zumunta da kuma musayar al-adu da korewa tsakanin sojojin wadannan kasashe.
Boris Burmistrov, karamin jakadan kasar Rasha a birnin Esfahan ya ce an fara gudanar da irin wannan gasar tsakanin sojojin wadannan kasashen ne, shekaru 7 da suka gabata a kasar Rasha. Jakadan ya ce a wannan karon sojoji ‘yan wasa 730 daga kasashen Rasha, Vetnam, Uzbekistan da kuma Iran ne suke halattar gasar.
Bumistrov ya kammala da cewa za’a ci gaba wasannin daga jiya Lahadi har zuwa 2 ga watan satumba mai kamawa.
342/