15 Agusta 2021 - 12:47
Ra’isi : An Kammala Shirin Shigo Da Riga Kafin Korona Miliyan 30Ra’isi : An Kammala Shirin Shigo Da Riga Kafin Korona Miliyan 30

Shugaban kasar Iran, Ibrahim Ra’isi ya ce gwamnatinsa za ta baiwa batun yaki da cutar korona fifiko sosai.

ABNA24 : A cewar shugaban kasar, komi ya kammala a shirin shigo da alluran riga kafin cutar miliyan talatin.

A don haka dukkan bangarori na gwamnati da masu zaman kansu da sauren bangarorin al’umma na kasar ya kamata su bada hadin kai domin yaki da wannan cuta mai hadarin gaske.

Kwararu sun bayyana cewa ana bukatar karin alluran miliyan 60 domin shako kan annobar ta koron a kasar.

342/