11 Agusta 2021 - 13:33
Najeriya Za Ta Dawo Da Yin Rigakafin COVID-19 A Ranar 16 Ga Watan Augusta

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za a dawo da yin rigakafin cutar nan ta COVID-19 a ranar 16 ga watan Augustan bayan ta samu kimanin allurar rigakafin miliyan 4 wanda ake sa ran za su iso ƙasar.

ABNA24 : Shugaban hukumar kiwon lafiya ta ƙasar Faisal Shu’aib ne ya sanar da hakan inda ya ce ana ci gaba da tsattsara allurar rigakafin waɗanda suka iso ƙasar daga Amurka don fara aiwatar da shirin rigakafin.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Najeriyan ta sanar da dakatar da yin rigakafin wanda ta ce za ta sanar da lokacin da za a dawo yi, ana ganin ƙarancin alluran rigakafin ne ya sanya aka dakatar ɗin.

Ya zuwa yanzu dai wani ɗan adadi ne na mutanen ƙasar da suka ƙetare miliyan 200 suka samu aka yi musu allurar saboda ƙarancin allurar. Wasu ƙididdigar dai sun nuna cewa mutane miliyan biyu ne suka samu yin allurar rigakafin sau ɗaya ƙasar, alhali wasu 700,000 kuma suka samu damar yin duka biyun.

Cikin ‘yan kwanakin nan dai ana ci gaba da samun ƙaruwar masu mutuwa da kuma kamuwa da cutar ta Korona inda ya zuwa yanzu dai kimanin mutane 175,000 suka kamu da cutar a ƙasar kana wasu sama da 2000 kuma suka mutu.

342/