9 Agusta 2021 - 14:39
Hizbullah: Amurka Ba Zata Iya Raba Mutanen Kasar Lebanon Da Kungiyar Ba

Shugaban majalisar gudanarwa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa Amurka da sauran makiyan kungiyar, masu neman fitina ba za su iya raba ta da mutanen kasar ba.

ABNA24 : Kafar watsa labaran ‘Al-Ahad’ ta nakalto Sayyid Hashim Safiyyuddin yana fadar haka, ya kuma kara da cewa mutanen da suka yi hakuri da kungiyar Hizbullah na tsawon shekaru fiye da 30 sun ga kuma yadda ta sadaukar da kanta wajen kare kasar daga makiyanta, da sauki haka ba za su kyale ta ba.

Safiyyudin ya kara da cewa kasashen Saudiya da Amurka sun kashe dalar Amurka kimanin biliyan 20 don bata sunan kungiyar da kuma rusa ta, amma sun kasa cimma hakan.

Daga karshe shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar ya kammala da cewa dole ne mutanen kasar Lebanon su gane kan cewa Amurka wacce ta ke goyon bayan HKI ita makiyar kasar ta gaskiya, don dukkan matsaloli na tattalin arzikin da kasar ta fada ciki ita ce da haddasa su.

342/