ABNA24 : Fashewar wacce ta auku a ranar 4 ga watan Agustan 2020, ta sanadin mutum 191 tare da jikkata wasu 6,000 a cewar alkalumman hukumomin kasar suk afitar a watan Satumban bara.
Har yanzu kuma akwai mutanen da ba’a gan su ba, bayan aukuwar lamarin.
Ko baya ga hakan fashewar ta ruguza dimbin gine gine a birnin na Beirut.
An bayyana cewa fiye tan da 2,750 na wasu sinadirai na Ammonium nitrate da aka ajiye a wani wajen ajiye kayayyaki na tsawon shekaru shida ne ya janwo wannan barna.
Aukuwar lamarin dai ya kara jefa kasar cikin matsin tattalin arziki da rikicin siyasa da ba’a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar.
342/