24 Yuli 2021 - 06:27
​Pakistan Ta Bukaci MDD Ta Gudanar Da Bincike Don Tabbatar Da Ko India Ta Yi Satar Maganganun Imran Khan

An sami lambar woyar firai ministan kasar Pakistan Imran Khan a cikin jerin lambobin da ake zaton HKI ta yi amfani da manhajin nan ta Pegasus don maganarsa tun shekara ta 2016 a lokacinda manhajin ya fara aiki.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a ranar Lahadi 17 ga watan yuli da muke ciki ne wasu kamfanonin kasa da kasa suka a yayin bincike suka tabbatar da cewa sun taimakawa yahudawan wajen aikin satar bayanai a wayoyin shuwagabannin kasashen duniya da manya –manyan mutane da kuma wasu fitattun mutane a duniya.

A jiya jumma ce ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta zargi kasar india da amfani da irin wadan nan ayyukan leken asiri.

Labarin ya kara da cewa al-amarin ya shafi shugaban kasar Faransa da ministocinsa wadanda suka canza wayoyi da lambobinsu a jiya.

342/