ABNA24 : Sayyid Ra’isi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen fadar ta Vatican Cardinal Pietro Parolin a yayin bikin babbar salla inda ya bayyana cewar ya kamata a ɗauki ranakun bukukuwan Musulunci a matsayin wasu ranaku na haɗin kai da aiki tare tsakanin saukakkun addinai kana kuma wata hanya ta ƙaddamar da tattaunawa tsakaninsu.
Ra’isi ya ci gaba da cewa siyasar cikin gida da ta waje ta Iran ta ginu ne bisa kare haƙƙoƙin bil’adama don haka ƙasar tana maraba duk wata tattaunawa da musayen ra’ayi tsakanin saukakkun addinai musamman addinin Kiristanci.
Don haka sai ya ce wannan siyasa ta kare haƙƙoƙin bil’adama ce ma ta sanya Iran ɗin goyon bayan Falasɗinawa kan mamayar Isra’ila, goyon bayan al’ummar Yemen a kan wuce gona da irin Saudiyya a kan al’ummar ƙasar bugu da ƙari kan taimakon ƙasashen Iraƙi da Siriya wajen faɗa da ta’addanci.
Sayyid Ra’isi ya ce: Na yi amanna da cewa Iran da Vatican, bisa koyarwar saukakkun addinai za su iya taimakon waɗanda ake zalunta a duniya da kuma faɗa da ma’abota girman kai.
Zaɓaɓɓen shugaban na Iran ya ce a halin yanzu ya kamata kare haƙƙoƙin bil’adama ya zamanto tushen haɗin kai da aiki tare tsakanin saukakkun addinai ciki kuwa har da Musulunci da Kiristanci.
Shi ma a nasa ɓangaren sakataren harkokin wajen fadar ta Vatican Cardinal Pietro Parolin ya ce ya kamata saukakkun addini sun ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dunyiya, yana mai fatan Iran da Vatican ɗin za su ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu.
342/