ABNA24 : Rahotannin sun ce an kai harin ne a ƙoƙarin waɗanda suka kai hari na kashe wani babban jami’in ‘yan sandan ƙasar.
Yayin da yake magana kan harin wanda aka kai shi a yankin Benadir, da ke birnin na Mogadishu, kakakin ‘yan sandan ƙasar Somaliyan Sadiiq Dudishe ya ce an kai harin ne kan ayarin motocin kwamishinan ‘yan sandan yankin Kanar Farhan Mohamudu Qaroleh, sai dai ya tsira da ransa.
Kakakin ya ce wani ɗan ƙunar baƙin wake ne da yayi jigida da bama-bamai ya kai harin a ɗaya daga cikin titunan da ke cike da mutane a babban birnin, inda ya ce mutane 9 sun rasa rayukansu sannan wasu da dama kuma sun sami raunuka waɗanda suke ci gaba da shan magani a asibitoci daban-daban na birnin.
Кungiyar ta’addancin nan ta Al-Shabab da ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qa’ida ta ɗauki alhakin kai wannan harin.
Tun a shekara ta 2007 ne dai ƙungiyar al-Shabab ɗin ta ƙaddamar da hare-hare kan gwamnatin Somaliyan da jami’anta musamman jami’an tsaro da kuma sauran fararen hula da sunan ƙoƙarin kafa gwamnatin Musulunci.
342/