ABNA24 : A zaman na ranar Alhamis, dukkan lauyoyin masu gabatar da kara da wadanda ake kara sun yi wa kotu bayani.
Babban lauya ga Malam El-Zakzaky, Femi Falana, wanda ya yi magana da manema labarai jim kadan bayan dage zaman, ya roki Kotun da ta yanke hukunci a kan wadanda yake karewa.
Tun a shekara ta 2015 ne dai ake tsare da malamin, da maidakinsa bayan farmakin Zariya.
342/