1 Yuli 2021 - 11:52
An Harbe Wasu Masu Zanga-Zanga Biyu Da Raunata Wasu Na Daban A Кasar Ghana

Rahotanni daga ƙasar Ghana sun bayyana cewa an bindige wasu masu zanga-zanga guda biyu da kuma raunata wasu guda huɗu yayin fito na fito da jami’an tsaro a yankin Ashanti na ke kudancin ƙasar ta Ghana.

ABNA24 : Rikicin dai ya faro ne tun ranar Talata lokacin da mutane garin Ejura sun taru don nuna rashin amincewarsu da kisan gillan da aka yi wa wani matashi mai fafutuka kana kuma memba a sabon yunƙuri gyara da aka ba shi sunan #FixTheCountry Ibrahim ‘Kaaka’ Mohammed.

Rahotanni sun ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun yi amfani da ƙarfin tuwo wajen kawo ƙarshen zanga-zangar da al’umma suka yi inda mutane biyu suka rasa rayukansu, kamar yadda kakakin ‘yan sandan Godwin Ahianyo ya shaida wa manema labarai wanda ya ce tuni an samu nasarar kwantar da rikicin.

Har ila yau ‘yan sandan sun ce sun kama mutane biyu da ake zargi da hannu cikin kisan gillan da aka yi Ibrahim Kaaka ɗin wanda ya kasance daga cikin masu tsananin sukar gwamnatin ƙasar ta Ghana.

342/