ABNA24 : Sakamakon kuri’ar jin ra’yin ya nuna cewa dan takarar shugaban kasa Ibrahim Ra’isi kuma alkalin alkalan kasar , shi ne a gaba da kimani kashi 57% na kuri’un da za’a kada.
Prestv ta kara da cewa an sami wannan sauyin ne bayan da ‘yan takarar neman kujerar shugabancin kasar 3 suka janye daga takarar.
Biye da shi akwai Muhsen Razae tare da kashi 5.8%, sai Naser Himmati da kashi 2.8%, sai Amir Husain Hashimi da kashi 2.2%.
Har’ila yau akwai kashi 18.3% na masu zabe wadanda har yanzu basu tsaida dan takarar da zasu zaba ba.
342/