ABNA24 : Rauhani ya ce, fitowa zabe ga dukkanin 'yan kasa yana a matsayin wata babbar amsa ce ga makiya, wadanda suke hankoron ganin sun mayar da kasar saniyar ware a duniya, bisa hujjar rashin sahihiyar demukradiyya, ko rashin bai wa 'yan kasa hakkokinsu na zabe. Daga karshe Rauhani ya fatan alhairi ga dukkanin 'yan kasarsa, da kuma fatan ganin komai ya gudana bisa tsari da kiyaye ka'idoji da doka da oda.
342/