20 Satumba 2026 - 23:31
Source: ABNA24
Menene Manufar Halittar Ɗan Adam A "Tsarin Shari'a"?

Allah Mai Hikima ne kuma ba ya yin aiki maras hadafi haka akwai face yana da manufa. Manufar halittar aljannu da mutane a tsarin shari'a shine don su kai ga kamala ta hanyar ibada kuma idan mutum wanda yake da ruhu mai zaman kansa na hankali ya bunƙasa shi ha rya tserewa abokansa, shi kansa zai zama manufa ga halittu da dama na ƙasa da shi. Ibada tana da matakai da yawa waɗanda wasu manufa ce ta tsakiya wasu kuma manufa ce ta ƙarshe. Alkur'ani yana ɗaukar manufar halittar duniya ita ce sanin mutum ga ikon Allah da iliminsa maras iyaka; don haka, tabbaci na gani (yaqin shuhudi) ga ilimai, ita ce manufar ƙarshe ta halittar mutum wadda koyaushe ta dogara kan ibada.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa da Ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA: Sakamakon hikimar Allah Maɗaukaki, babu wani aiki na kawai da ke fitowa daga gare shi; domin Allah Mai Hikima ne kuma kowane mai hikima yana yin aikinsa da manufa; don haka aikin Allah yana da manufa (1) kuma saboda wadatarsa ta asali babu wani abu da zai iya zama manufa ga zatinsa(2); domin abin da ake buƙata shi ne cewa zatin Allah ba zai zama cikakke ba ba tare da wannan manufar ba kuma da samun ta zai zama cikakke yayin da Wajibul-Wujud ainihin kamala ce tsantsa maras iyaka da ba a yi tunanin wata kamala sabaninta a zatinsa. Haɗa waɗannan manufofi biyun yana buƙatar cewa wanda ya samar da duniya, ya tsarkaka daga manufa — domin shi kansa ainihin manufar kowace halitta ne kamar yadda shi ne ainihin mafarin kowace wanzuwa — duk da duniyar kanta tana da manufar wanzuwa kuma za ta same ta, ko da yake wasu daga cikinta ba za su tsira daga mummunan haɗari akan hanya ba.

Manufar halittar aljannu da mutane a tsarin shari'a shine don su kai ga kamala ta hanyar ibada kuma idan mutum wanda yake da ruhu mai zaman kansa na hankali ya bunƙasa shi ha rya tserewa abokansa, shi kansa zai zama manufa ga halittu da dama na ƙasa da shi, ko da yake manufar ƙarshe ta kowa ita ce Allah; amma kamar yadda a cikin (Qausu Nuzul) - tsarin saukowar halitta daga Allah zuwa duniya-, wanda farkon abin da ya fito daga gareshi shine jigon hankali, wanda a cikin tsarin (Qausu Su’ud) -tsarin komawar halitta daga duniya zuwa ga Allah- ya zamo cikakken mai komawa shine jigon mai hankali, Tafiyar ta fara ne daga hankali kuma ta ƙare da mai hankali kuma wannan batu ba ya kan tunanin hankula goma da makamantansu wanda hikimar "Masha" ma ba ta ɗauke shi a matsayin wani batu tabbatacce na falsafarta ba ta ambace shi a matsayin abu mai yiwuwa kawai; sai dai yana kan tushen bayyanuwar Allah a matakai daban-daban na wanzuwa ko bayyanuwa wanda hikimar maɗaukakiya ko irfani ke fahimta ko yake iya gani.

Ibada tana da matakai da yawa waɗanda wasu manufa ce ta tsakiya wasu kuma manufa ce ta ƙarshe, tunda aiki iyaka ne kuma ganin hakika da zuciya maras iyaka ne, ayyukan ibadun manufofi ne masu iyaka kuma ibadun ganin hakika da zuciya manufofi ce maras iyaka kuma hikimar iyakancewar ayyukan ibadun shi ne cewa nauyin wajibi ya ƙare ta hanyar yin ƙaura daga duniya zuwa lahira; amma fagen gani na zuciya yana ci gaba kuma ci gaban aiki da ake samu ta zabin aikin mutum, ba ya cikin ranar tashin kiyama; amma ci gaban ilimi da ake samu ta hanyar saukakawar Allah Maɗaukaki, koyaushe yana yiwuwa kuma da yawa daga cikin labulen gaibu za su bayyana bayan mutuwa domin abin da ba a gani ya zama abin da ake iya gani. Don haka Alkur'ani Mai Girma yana ɗaukar manufar halittar duniya ita ce sanin mutum ga ikon Allah da iliminsa maras iyaka:

«اللَّهُ الَّذی خَلَقَ سَبْعَ سَماواتٍ وَ مِنَ الْأَرْضِ مِثْلَهُنَّ یَتَنَزَّلُ الْأَمْرُ بَیْنَهُنَّ لِتَعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ عَلی‌ کُلِّ شَیْ‌ءٍ قَدیرٌ وَ أَنَّ اللَّهَ قَدْ أَحاطَ بِکُلِّ شَیْ‌ءٍ عِلْماً»

"Allah shine wanda ya halicci sammai bakwai da kuma daga ƙasa misalinsu; umarni yana sauka a tsakaninsu domin ku sani cewa Allah kan kowane abu Mai Ƙarfi ne kuma cewa Allah yana kewaye ilimin kowane abu " (3).

Ko da yake ilimin da ake samu da tabbaci na dalili a matakinsa, ana ɗaukar su a matsayin kamalar ilimi kuma an sanya su a manufa, amma dangane da ilimin da ake samu da tabbaci na gani ana ɗaukar su kayan aiki ne:

«کَلاَّ لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ الْیَقینِ * لَتَرَوُنَّ الْجَحیمَ * ثُمَّ لَتَرَوُنَّها عَیْنَ الْیَقینِ» (۴)

"A'a, da kuna sani ga tabbacen ilimin * Da za ku ga jahannama * Sannan da za ku gan ta da tabbacin idon " (4) wato da tabbacen ilimi za a iya kaiwa ga Hakikar Yakini.

Don haka, ana iya ɗaukar tabbaci na gani ga ilimai a matsayin manufar ƙarshe ta halittar mutum wadda koyaushe ta dogara kan ibada, ko da yake yadda take dogara kan ibada a kowane mataki ya dace da wannan mataki wato a duniya tana dogara kan ainihin ibadun da aka shari'anta kuma a lahira tana bayyana da dogara ne ga abinda ya boyu na wanna ayyukan ibada, kuma idan wani lokaci ba’ai ibada  ba tom abin da ake gani zai ɓuya kuma wanda ke boye zai faku; domin kayan aikin gani na mai tafiya da bayyanuwar gaibu, ita ce ibada: "Kuma ka bauta wa Ubangijinka har tabbaci ya zo maka" (5)

«وَ اعْبُدْ رَبَّکَ حَتَّی یَأْتِیَکَ الْیَقینُ» (۵)

Ba wai bayan tabbaci bauta ta ƙare ba ne; saboda ɓacewar ibada ita ce ɓacewar tabbaci; domin sabo shine mafi munin labule.

Abin da ke fitowa daga aya ta 12 na suratul "Talaq" shi ne cewa manufar samuwar duniya, wato bayyanuwar gaskiya a madubin halitta, ita ce mutum mai tafiya ga ilimi ya samu sanin da ikon gaskiya kuma wannan ilimin gani ne a zuciya, yana mayar da mai irfani wanda ya isa ya zama bayyanar "Mai Ilimi" da "Mai Ƙarfi" wanda da "Bismillahir Rahmanir Rahim" idan Allah Maɗaukaki ya ba da izini, zai iya yin aiki a duniya irin aikin da yake yi a lahira da yayi niyya kawai kuma duk abin da yake so ya sani, yana gani.

Ana iya fito da wannan batu daga sanannen hadisi mai tsarki cewa amfanin bayyanuwar zati wanda taska ce ta ɓoye (bayyanuwar zati ita ce bayyanuwar gaskiya a madubin gaskiya) ita ce sanin mutum mai tafiya cikin gaibu cikakke gwargwadon ƙarfinsa kuma idan akwai magana a cikin sanadin hadisin da aka ambata, aya ta suratul "Talaq" tana ba da garantin abin da yake ciki; domin ayar da aka ambata tana ɗaukar ilimi a matsayin manufar halitta da kuma iko kuma tunda ikon Allah ainihin iliminsa ne, ikon mutum mai irfani ma yana cikin wannan ilimin ne; domin hankali na aiki da na nazari a cikin masu tafiya abin haɗuwa ne.

Madogara:

(1). Suratul Mu'minun, aya ta 115.

(2). Suratul Ibrahim, aya ta 8.

(3). Suratul Talaq, aya ta 12.

(4). Suratul Takathur, ayoyi 5-7.

(5). Suratul Hijr, aya ta 99.

(6). An tattaro bayanan daga littafin: Hikmat al-Ibadat, Javadi Amoli, Abdullah, mai bincike: Shafi'i, Hussein, Cibiyar Bugawa ta Isra, Qom, 1388 Hijira ta Rana, bugu na goma sha biyar, shafi 23.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha